Fadar shugaban ?asa ta ce babu ?amshin gaskiya cikin kalaman da ake ya?awa kan cewa Muhammadu Buhari na shirin mi?a mulki ga gwamnatin ri?on ?warya.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC, mataimaki na musamman ga shugaban ?asa kan lamuran ya?a labarai Malam Garba Shehu ya ce, “ya kamata a daina ?aukar lamarin gwamnatin ri?o da wasa, maganar za?e na nan daram.”
Yayin da aka jiyo wasu shugabannin na zargin cewa Shugaba Buhari na neman da?ile kafafun dimokradiyyar Najeriya, a wani gefen kuma i?irari ne kan cewa ?arancin naira da ake fama da shi a Najeriya wani ?angare ne na janyo koma baya ga za?e mai zuwa da za a gabatar nan da kwanaki, da kuma shirin mi?a iko ga gwamnatin ri?o.
A nasa martanin kakakin shugaban ?asar ya ce wannan wani salo ne mai cike da ha?ari da wasu mutane suka ?auka wa?anda suke ganin za su iya fa?uwa za?en.
Ya ?ara da cewa ?ir?iro yanayin da zai jefa mutane cikin firgici ba hanya ba ce da za ta kawo ?arshen damuwar da aka shiga ba ta sauyin naira.
Yace sauyin ku?in ba a ?ir?iro shi ba ne domin ya bai wa shugaban ?asa damar zama a kan karagar mulki har bayan 29 ga watan Mayu, yana cewa “fadar shugaban ?asa a shirye take ta mi?a mulki ga duk wanda ya ci za?e domin gadar Shugaba Buhari.
Kuma za a yi hakan ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
