DPO Ya Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Shugaban ofishin ?an sanda na ?aramar hukumar Takai ya lashe gasar izu 60 ta karatun Al Kur’ani mai tsarki da aka rundunar ?an sandan jihar Kano ta shirya.

DPO Mahi Ahmad Ali, ya zo na ?aya ne a gasar ajin izu 60, inda ya samu kyaututuka da dama da suka hada da ku?i da kyayyaki na amfanin yau da kullum.

Gasar wacce aka kammala a ranar Alhamis ita ce irin ta farko da rundunar ?an sandan Kano ta gudanar ga jami’nta.

?an sanda kusan 39 ne suka shiga musaba?ar ta Al Kur’ani ta kwana biyu kuma wadanda suka shiga musaba?ar sun samu kyaututuka daban daban.

Kakakin rundunar ?an sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce gasar ta ?an sanda ce zalla kuma gasar ta ?unshi izu biyu da izu biyar da 10 zuwa 20 da masu izu 40 da 60

Sai dai gasar ta maza ce zalla ba mata amma rundunar yan sandan Kano ta ce saboda wannan ne karon farko, tana fatan a gaba za a ?ara shiri.

SP Mahi Ahmad Ali shugaban ?an sanda mai kula da ?aramar hukumar Takai da ke Kano shi ne wanda ya lashe gasar Al Kurani ta izifi 60.

Bayan lashe gasar ya yi godiya ga Allah inda ya ce wannan wata dama ce ta ?ara inganta karatunsa na Al Kur’ani.

“Aikinsa na ?an sanda bai hana ni tilawar Kur’ani ba,” in ji shi.

Kadif Abubakar Abdullahi Usman daga kwalejin ?an sanda ta Wudil ne ya zo na biyu a karatun izu 60 yayin da sufeto Ibrahim Abubakar da ke aiki a hedikwatar yan sanda da ke Bompai ya zo na uku.

Related posts

Leave a Comment