Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Antoni Janar na ?asar nan kuma ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya musanta rahoton dake cewa ya bayyana sha’awar neman kujerar gwamnan Kebbi a shekarar za?e ta 2023.
A wata sanarwa da babban mai taimaka wa Ministan kan harkokin ya?a labarai, Dakta Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar a madadin Malami ya musanta rahoton inda yace labarin ?anzon kurege ne.
Sanarwan mai taken, “Har yanzun ban bayyana shiga takara ba – Malami,” ta ce karin haske kan lamarin ya zama wajibi duba da wasu kafafe sun fara ya?a jita-jitar.
Wani sashin sanarwan ya ce: “Gwandu ya ce lamarin ayyana shiga tseren wata kujerar siyasa ba harka ce da za’a yi ta a du?unkune ba ko wani bangaren kafafen watsa labarai ne ka?ai za su yibrahoto ba.”
“Rahoton ya samo asali ne daga son asani da kuma ?osawar masoya da masu goyon baya da suka ?agara.” “Gwandu ya ce idan lokacin da ya dace ya yi, za su ji daga bakin mai gayya mai aiki da kansa da kuma dukkan kafafe, masu ruwa da tsaki, masoya, mambobin jam’iyya da tawagar magoya baya.”
Malami, wanda ?an asalin jigar Kebbi ne, ya shafe wa’adi biyu a matsayin mamban gwamnatin shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, kuma babban jigon jam’iyyar APC.
