Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babban Hafsan Sojojin Najeriya Faruk Yahaya, ya sake jaddada aniyar Rundunar Sojojin Najeriya ta ganin cewa wajibin su ne su mur?ushe duk wasu masu kawo tashin hankali a fa?in ?asar nan.
Laftanar Janar Yahaya ya bayar da wannan tabbacin a wurin wani taron da aka gudanar a Hedikwatar Ofishin Sojojin Najeriya a Abuja, ranar Talata.
Manjo Janar Anthony Omozoje Shugaban Sashen Tsare-tsare ne ya wakilci Faruk a wurin taron.
Ya ce yawaitar tashe-tashen hankula a ?asar nan sun sa ana bibiya da canja takun tsarin da?ile bazazanar tsaro a kai a kai.
Ya ce ayyukan ‘yan ta”adda, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga na ci gaba da kawo barazana ga ?asar nan.
Ya ce barazanar ta kuma shafi har sojojin Najeriya.
Tun da farko dai Babban Jami’in Soja mai kula da fannin sufuri da ?ir?ira, Charles Ofoche ya ce taron kara wa juna ilmin da aka tsara, an yi shi ne domin a ?ara zaburar da dakarun da ke bakin fagen daga, kana gwabza ya?i a Arewa maso Gabas da sauran yankunan da ake tashin hankula.
Faruk ya ce sojojin Najeriya na ?o?ari sosai wajen gaggauta yi wa masu kai hare-hare dirar-mikiya.
Ya ce su na samun nasarori sosai, duk kuwa da irin ?alubalen fa?a?a da matsalar tsaro ke yi a yankuna daban-daban.
Idan ba a manta ba, Najeriya ta samu kan ta cikin gagarimar matsalar Boko Haram, ya?in da ya gagari ‘yan sanda, sai dai ake amfani da sojoji fiye da shekaru 10.
Haka nan ma an zuba sojoji wajen ganin an da?ile hare-haren ‘yan bindiga, wa?anda su ma suka gagari ‘yan sanda.
Yamutsi da tayar da ?ayar bayan da tsagerun IPOB ke yi a Kudu maso Gabas shi ma ya yi munin da sai da Najeriya ta tura dakarun sojojin ta a yankin.
