Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar maii ?akin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce a ganinta babu bu?atar shugabannin Najeriya su fita waje don neman lafiya bayan kaddamar da kaddamar da asibitin fadar shugaban ?asa wanda ya la?ume ku?i naira biliyan 21.
Aisha Buhari ta bayyana haka ne lokacin da bi sahun shugaba Muhammadu Buhari da sauran mu?arabban gwamnati wajen kaddamar da asibitin da ke cikin fadar shugaban ?asa a Abuja a ranar Juma’a.
Matar shugaban ?asar Najeriyar ta fa?a wa manema labarai cewa ta bijiro da batun ganin an samar da asibitin ne shekara shida da suka gabata, bayan ?aukar tsawon lokaci da mijinta ya yi a waje domin neman lafiya.
Ta tabbatar da cewa ganin an samar da asibitin a yanzu, shugabannin ?asar da iyalansu ba sa bu?atar fita waje neman lafiya, sai dai su kawo ?wararrun likitoci domin taimaka wa takwarorinsu na ?asar.
