Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar EFCC mai ya?i da cin hanci da rashawa ta ce wasu ‘yan siyasa da take zargi da rashawa na ?o?arin ficewa daga ?asar kafin su sauka daga mulki ranar 29 ga watan Mayu.
EFCC ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani ga Gwamnan Zamfara Bello Matawalle game da zargin da ya yi wa shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa cewa ya nemi rashawar dala miliyan biyu a hannunsa – kwatankwacin naira miliyan 922.
“Idan har Matawalle da gaske yake, ya kamata ya daina ?a?atu ya gabatar da hujja ?arara kan zargin da yake yi,” in ji wata sanarwa da EFCC ta wallafa ranar Juma’a.
Ta ?ara da cewa: “Kazalika, hukumar na ankarar da al’umma cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa da ke shirin ficewa daga Najeriya kafin ranar 29 ga watan Mayu.”
EFCC ta ce Gwamna Matawalle ya fara gabatar da zarge-zargen ne bayan ta ?addamar da bincike kan zargin almundahanar naira biliyan 70 a kansa na wasu ayyukan da ta ce an bayar amma ‘yan kwangilar ba su yi ba.
Bello Matawalle na jam’iyyar APC mai mulkin ?asar na cikin gwamnonin da za su sauka daga mulki a ranar 29 ga Mayu bayan ya sha kaye a hannun Dauda Lawal na PDP a za?en watan Maris da ya gabata.
