?ungiyar maya?an ISWAP mai i?irarin jihadi ta yi i?irarin cewa ta kashe maya?an sa-kai uku da ke aiki da rundunar sojan Najeriya a Jihar Borno.
Kazalika, ta ce ta yi garkuwa da wasu ma’aikatan agaji na ?ungiyar Red Cross yayin harin da ta ce ta kai ranar Juma’a.
?ungiyar ta bayyana hakan ne ciikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na dandalin Telegram ranar Asabar, tana mai cewa ta kai harin ne a garin Monguno.
A watan Agustan 2020 ne ?ungiyar ta ayyana ya?i a kan ma’aikatan agaji da ke aiki a Jihar Borno, tana mai zargin su da aiwatar da ayyukan “rusa Musulunci”
