Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu gungun ‘Yan bindiga ?auke da muggan makamai sun halaka manoma 11 a yankin Ghandi dake karamar hukumar Rabah ta jihar.
Kamar yadda bincike ya nuna, harin ya faru wurin karfe 12 na ranar Asabar. Wata majiya tace wadanda lamarin ya ritsa dasu suna aiki ne a gonakinsu yayin da aka kai musu farmakin.
KARA KARANTA WANNAN Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kone Ofishin ‘Yan Sanda, Shaguna da Gidaje a Bukkuyum Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Halaka Manoma 11, Sun Kallafawa Wasu Harajin Noma. Hoto daga thecable.ng Asali: UGC LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Sun riske su a gonakinsu kuma suka kashesu babu dalili,” sakataren hakimin Ghandi, Tukur Muhammad, ya sanar da Daily Trust. ‘Yan bindigan sun yi yunkurin garkuwa da wasu manoman amma ‘yan sa kai suka bankado shirinsu.
Muhammad ya bayyana cewa, takwas daga cikin manoman an kashe su a kauyen Kuryar yayin da uku aka halaka su a kauye mai makwabtaka. “Basu son mu yi aiki a gonakinmu. A kowacce rana suna kai wa manomanmu farmaki.
Sun kuma bukaci sauran kauyukan da su biya haraji kafin su bar su yin noma duk da ba da wannan muka dogara ba a yankinmu,”
A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ya ce yana kan hanya ne amma zai bincika kuma ya kira, wanda har a lokacin rubuta wannan rahoton bai yi ba.
