Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufai ya bayar da shawarar a ?ona dazukan arewa domin ?akkabe ?arayin daji da suka addabi yankin.
“Na sha fa?a cewa, abin da ya kamata shi ne a ?ona dajin, a kashe su gaba ?aya, daga baya mu sake shuka bishiyoyi,” kamar yadda gwamna El-Rufai ya shaidawa kafar Arise TV a wata hira ta musamman.
Ya ?ara da cewa ?ona dajin ne kawai mafita duk da matakin zai shafi wa?anda ba su ji ba su gani ba.
“Ya fi a kakkabe su a dawo da zaman lafiya mutane su koma noma,” in ji shi.
Ya ce yadda ake tunkararsu ba zai kawo ?arshen matsalar ba – “domin idan an kore su daga Sokoto, za su tsere su tsallaka Kebbi.”
“Abin da za a yi kawai a yi masu ruwan wuta ta sama da ?asa a dukkanin jihohi shida na arewa maso yammaci da Neja.”
“Idan aka yi haka ina ganin cikin makwanni ana iya maganin matsalar ”
