An Bankado Yadda Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya Suka Jidi Naira Tiriliyan 13.95 Ba Bisa Ka’ida Ba

IMG 20240308 WA0066

A?alla Naira tiriliyan 13.95 ne Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati suka jida ba bisa ?a’idar da Kundin Dokokin Najeriya ya shar’anta ba.

Rahoton da Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya fitar ne kan yadda hukumomin gwamnati suka kashe ku?a?e a shekarar 2020.

Rahoton ya fallasa cewa jidar ku?a?en ba bisa ?a’ida ba ya kawo na?asu da tawaya wajen kasa tantance daidaiton gano ku?a?en da aka fitar aka yi aiki da su har Naira 13,955,069,757,335.00.

Wannan gurungun?uma dai ta karya Dokar Ku?a?en Gwamnati ta 2009, wadda ta ce “Kada gwamnati ta ciri ku?i daga asusun bankuna kai-tsaye. Idan kuma aka cira, to ma’ajin hukumar ko ma’aikatar zai fuskanci hukuncin biyan ku?a?en bankin zai caja.”

Sai dai kuma wata sabalula da asar?ala ita ce an bayyana ku?a?en a matsayin aro da ayyukan ha??in gwamnati.

Ma’aikatar Muhalli ce aka fi yin wannan karya doka, inda aka jidi Naira biliyan 350.85.

Mai bi mata ita ce Hukumar Binciken Ingancin Abincin da ake Ajiyewa, wato Nigeria Stored Products Research Institute,

Ofishin Biyan Ku?a?en Gwamnatin Tarayya da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, wanda ya jide Naira biliyan 27.95.

Benin da Ilorin ne na su adadin da aka jida na su da yawa, kama daga Naira biliyan 107.50 jimlace.

Mai Binciken Kudi na Gwamnatin Tarayya Shaakaa Chira ya ce an jide wadannan ku?a?e ba tare da sahalewar gwamnati ba.

?arin abin mamaki kuma shi ne duk ba su yi bayanin ayyukan da aka yi da ku?in ba.

Chira ya ce karkatar da ku?a?en ya faru ne saboda rashin ka??arfar masu sa-ido kan adadin ku?a?en da ma’aikatu za su fitar.

Tsarin fitar da ku?a?en gwamnatin tarayya ya ?ara da cewa ya gano ma?asudin ?in bin ?a’ada wajen cirar ku?a?e ne saboda an ri?a watsa wasu ku?a?en cikin aljihun masu cirar ku?a?en.

Sai dai kuma wata ?wararriya kan sha’anin bin ?a’idar cirar ku?a?e mai suna Adenike Aloba, ta ce ya kamata a ?ara wa Ofishin Akanta Janar ?arfi, ba kawai ya tsaya ya na yin kira ko zare ido ka?ai, ka?ai ko cewa a maido da ku?a?en da gaggawa ka?ai.

Related posts

Leave a Comment