Adamawa: Gwamna Fintiri Ya Sanya Hannu A Kasafin Kudin 2022

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya sanya hannu akan kasafin kudin Shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu wanda ya kai sama da naira bilyan dari da sittin da uku.

Sanya hanun na zuwane bayan da majalisar dokokin jihar ta Adamawa ta amince da kasafin kudin da gwamna Fintiri ya gabatarwa majalisar a cikin watan sha daya na Shekara ta dubu biyu da ashirin da daya.

Da yake jawabi a lokacin da yake sa hannun gwamna Ahmadu Fintiri ya yabawa majalisar dokokin bisa yadda suka duba kasafin akan lokaci, ya kuma godewa al’ummar jihar bisa hadin kai da goyon baya da suke baiwa gwamnati.

Da wannan nema yake tabbatarwa al’ummar jihar cewa gwamnati zata yi dukkanin abinda ya dace domin samar da zaman lafiya dama cigaban jihar baki daya.

A zantawarsu da muryar ‘yanci wasu mazauna jihar Adamawa irinsu Abdulrahman Musa shugaban shugabanin matasa na jam’iyar PDP a jihar tare da Abdulkadir Musa sun bayyana farin ciknsu dangane da yadda aka sanya hannu akan kasafin kudin wanda acewarsu haka zai bada damar gudanar da ayyukan cigaban jihar baki daya.

Sun kuma shawarci mazauna jihar ta Adamawa da su kasance masu hada kansu da kuma kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a tsakanin al’umma, domin wanzar da zaman lafiya mai dorewa.

Related posts

Leave a Comment