Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar kwamitin ya?in neman za?en shugaban ?asa na jam’iyyar APC mai mulki ya bu?aci hukumar za?e ta ?asa ta bayyana wa al’umar ?asar adadin katunan za?en aka kar?a a fa?in ?asar, gabanin babban za?en da ke tafe ranar Asabar.
Daraktan shirye-shirye da sanya idanu kan za?e na kwamitin ya?in neman za?en shugaban ?asa na jam’iyyar, kuma ministan ayyuka da gidaje na ?asar Babatunde Raji Fasola ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gabatar ranar Talata a Abuja babban birnin ?asar.
Ya ce ya kamata INEC ta bayyana adadin katin za?e da kowacce jiha da ?aramar hukuma ta kar?a a ?asar.
Ya ?ara da cewa “Mun shirya, mun bai wa wakilan jam’iyyarmu horo, mun kammala shirinmu game da za?en, dan haka muke ganin ya kamata INEC ta bayyana wa ‘yan ?asa adadin mutanen da suka kar?i katin za?ensu”.
“Ina ganin yin hakan zai taimaka wajen tabbatar da inganci da sahihancin za?en. An fa?a mana adadin mutanen da suka yi rajistar za?e, amma ba a fa?a mana yawan wa?anda suka kar?i katunansu ba, dan haka ya kamata mu tambaya”.
A ranar Asabar mai zuwa ne dai INEC za ta gudanar da za?en shugaban ?asa da na ‘yan majalisun dokokin tarayya a fa?in ?asar.
