An Haramta Wa ‘Yan Kasa Da Shekara 18 Mallakar Layin Waya

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sabuwar dokar hukumar sadarwan Najeriya ta haramta yan kasa da shekaru 18 mallakar layukan waya a fadin kasar.

Hukumar NCC ta ce dokokin kafa ta sun bata karfin yin haka saboda haka daga yanzu za’a daina yiwa yan Najeriya masu shekaru kasa da 18 rijisan layukan waya kuma ba zasu iya mallakar SIM ba a Najeriya.

Hukumar sadarwan Najeriya NCC ta bayyana cewa wannan umurni na kunshe cikin sabuwar dokar rijistan layukan waya da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

A wallafar, hukumar ta umurci kamfanonin sadarwa daga yanzu kada su sake yiwa yan kasa da shekaru 18 rijista. A cewar sanarwar: “Wanda za’a iya wa rijista shine mutumin da bai da kasa da shekaru 18 kuma shine wanda zai iya mallakan layin waya kuma ya iya siyayya daga kamfanin sadarwa mai lasisi.”

Related posts

Leave a Comment