Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi (Dr.) Aisha Bala Mohammed ta bada gudumuwar tallafin mota da wasu kayan aiki irin na zamani ga hukumar Yan’Sanda ta Jihar Bauchi a wani mataki na ganin an dakile wan nan mummunan dabi’a na cin zarafin yara Jinsi da a birni da kauye
Aisha Bala ta kara da cewa Gwamnati ta kafa kwamitin da suke ta aiki tukuru, Kuma suna aiki kafada da kafada da wan nan bangaren na mata Yan’Sanda masu yaki da cin zarafin jinsi, tare da kirkiro wan nan doka da ake kira (VAPP LAW) a turance, tace kula da wan nan bangaren yana da muhimmanci sosai.
Uwar gida Gwamnan tayi nuni da cewa “ta Kirayi hukumar Yan’sandan da su rika taimaka wa wan nan bangaren domin su rika zakulu masu aikata laifin cin zarafin jinsin a lungu da sako a cikin al’umma.
Aisha tace, “Kayan aikin zai taimaka ma Jami’an tsaron da Kuma basu zarafin aiwatar da aikin su cikin tsarin da zai haifar da Da-mai Ido, tare da kuma tuhumar masu aikata laifin da mika su kotu don yi masu shari’a da yanke masu hukunci mai tsanani”.
A lokaci da yake amsar kayayyakin a shalkwatar Yan’sandan na Jihar Bauchi,. Kwamishinan Yan’Sanda Sylvester Abiodun Alabi, ya yaba ma matar Gwamnan da irin namijin kokarin da take yi don yaki da wan nan mummunan dabi’a, kana yace bazasu bar duk wanda ya shiga hanunsu ba akan aikata fyade da makamantansu ba.
“Yace zamu ci gaba da aiki babu Kama hannun yaro, saboda dama muna da hakkin da ya rataya a wuyan mu na ganin munkare lafiya da dukiyoyin al’umma a ko ina a fadin Jihar”
Daga karshe yayi godiya a madadin hukumar Yan’sandan da ma na bangaren mata Yan’Sanda masu kula da wan nan matsalar, a cewarsa wan nan karin karfin gwiwa ne na hakika.
Daga Adamu Shehu Bauchi
