Rahotannin dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar wata kotun ?aukaka kara a birnin ba Yola ta tabbatar da Aishatu Dahiru Binani a matsayin halastacciyar ‘yar takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar APC.
Kotun da mai shari’a Tanko Yusuf Hassan ya jagoranta ta yi watsi da hukuncin wata kotun tarayya da ya sauke takarar Aishatu Binani, da sanar da cewa APC ba ta da takara a za?en 2023.
A lokacin sanar da hukuncinsa, alkalin ya umarci a mi?a sunan Binani ga hukumar za?e mai zamanta wato INEC, a matsayin ‘yar takarar gwamnan APC a Adamawa.
