Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin Najeriya 36 sun ce sun yi mamakin yadda ?aramin Ministan Kasafin Ku?i da Tsare-Tsare na ?asar, Clem Agba ya zarge su da jefa Najeriya cikin talauci.
A watan Nuwamba ne Hukumar ?ididdiga ta Najeriya ta ce mutum miliyan 130 ne a ?asar ke fama da talauci, kusan kashi 63 cikin 100 na a’umar ?asar.
To sai dai a wata sanarwa da ?ungiyar gwamnonin ?asar suka fitar mai ?auke da sa hannun daraktan ya?a labaran ?ungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo, ta bayyana kalaman ministan da cewa abu ne da bai kamata ba, kuma babu kanshin gaskiya a cikin kalaman ministan.
Gwamnonin sun ce i?irarin – da ministan ya yi cewa gwamnonin sun yi watsi da al’ummar karkara – ba shi da tushe balle makama.
A cikin makon da ya gabata ne dai ?aramin ministan Kasafin Ku?i da Tsare-Tsare Clem Agba a wani taro da ya yi da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ya ?ora alhakin katutun talaucin da ke damun ?asar kan gwamnonin jihohi.
