Auren Wuri Ke Haddasa Matsalar Tsaro A Arewa – Sanata Odebiyi

Sanata mai Wakiltar Ogun ta Yamma ya bayyana damuwar sa akan yawaitar Kashe-Kashe, da ku?in fansa, da fya?e, da dukkanin matsalolin tsaro dake fuskantar yankin Arewa na Najeriya.

Ya bayyana wannan matsalar ta’addanci a matsayin Auren wuri wanda ya zamanto Al’adar yankin Arewa, yana mai cewa, sai an daina Auren Wuri, sannan za’a magance talauci.

Ya bayyana haka, a lokacin da yake bada gudunmawar shi a wajen ?udiri da aka gabatar mai taken “bu?atar dake akwai na magance kisan ?an ta’adda da sauran matsalolin tsaro a ?ananan Hukumomi na Wasagu-Danko da Sakaba na Jahar Kebbi,” wanda Sanata Bala Ibn’Nallah mai wakiltar Kebbi ta Kudu ya gabatar a ranar Laraba.

A gudunmuwar shi, Sanata Odebiyi ya bayyana cewar yawaitar matsalar tsaro a Arewa zai cigaba saboda wani mataki da aka ?auka na maganin matsalar, marar ?orewa, tana mai cewa magance matsalar tsaro a Arewa, sai an magance matsalar daga tushe.

A cewar sa “a lokacin da Auren wuri yana faruwa saboda talauci”, sai suka haifi yaro a wannan yanayi, da zaran ya girma, to ?an ta’adda sai su ?auke su aiki.

Sanatan ya koka kan yawaitar yara marasa zuwa Makaranta, yana mai cewa a shekaru 9 Najeriya ta samu mutane Miliyan 10.

Related posts

Leave a Comment