Sanata mai Wakiltar Ogun ta Yamma ya bayyana damuwar sa akan yawaitar Kashe-Kashe, da ku?in fansa, da fya?e, da dukkanin matsalolin tsaro dake fuskantar yankin Arewa na Najeriya.
Ya bayyana wannan matsalar taaddanci a matsayin Auren wuri wanda ya zamanto Aladar yankin Arewa, yana mai cewa, sai an daina Auren Wuri, sannan zaa magance talauci.
Ya bayyana haka, a lokacin da yake bada gudunmawar shi a wajen ?udiri da aka gabatar mai taken bu?atar dake akwai na magance kisan ?an taadda da sauran matsalolin tsaro a ?ananan Hukumomi na Wasagu-Danko da Sakaba na Jahar Kebbi, wanda Sanata Bala IbnNallah mai wakiltar Kebbi ta Kudu ya gabatar a ranar Laraba.
A gudunmuwar shi, Sanata Odebiyi ya bayyana cewar yawaitar matsalar tsaro a Arewa zai cigaba saboda wani mataki da aka ?auka na maganin matsalar, marar ?orewa, tana mai cewa magance matsalar tsaro a Arewa, sai an magance matsalar daga tushe.
A cewar sa a lokacin da Auren wuri yana faruwa saboda talauci, sai suka haifi yaro a wannan yanayi, da zaran ya girma, to ?an taadda sai su ?auke su aiki.
Sanatan ya koka kan yawaitar yara marasa zuwa Makaranta, yana mai cewa a shekaru 9 Najeriya ta samu mutane Miliyan 10.

