Zamfara: An Gurfanar Da Matan Da Ake Zargi Da Jefa Kur’ani A Masai

Rahotannin dake shigo mana daga ?aramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara na bayyana cewar an gurfanar da wasu mata uku gaban kotu Shari’a dake Gusau, babban birnin jihar kan zargin laifin wulakanta Al-Qur’ani mai girma.

Matan da ake tuhuma sun hada da Rabi Bello, Hazira Bello da Hafsatu Isah, duka yan garin Gada na karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara. Matan sun gurfana gaban Alkali Garba Sahabi Gusau.

Ana zarginsu da laifin sa wa AlQur’ani mai girma jinin haihuwa sannan suka jefar cikin masai.

Rahotanni sun bayyana cewar hujjojin da aka gabatar gaban kotu sun hada da AlQura’ni guda jike da jini, sirinjin jinin biki 77 da aka dauka bayan haihuwa, wasu littafai, takarda mai dauke da sunan daya cikin matan da kuma wasu abubuwan tsubbu da boka mai suna Tukur ya basu.

Lauyan Gwamnati ya bayyanawa kotu cewa matan na kokarin sihirin neman kudi ne ya sanya su kauce hanya. Alkalin ya dage zaman zuwa ranar 3 ga Maris .

Related posts

Leave a Comment