Labarin dake shigo mana daga Jihar Osun na bayyana cewar Mutane sun shiga tashin hankali biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kai ofishin da ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ke amfani da shi wajen yakin neman za?e.
An ruwaito cewa ministan na amfani da gidan Oranmiyan dake yankin Coca Cola, Osogbo jihar Osun, a matsayin ofishin ya?in neman za?e.
Rahotanni sun bayyana cewar ‘Yan bindiga sun dira yankin da misalin ?arfe 5:30 na yamma na ranar jiya Alhamis kuma nan take suka bu?e wa ginin ofishin wuta.
Rahoton da muka samu ya nuna cewa maharan sun harbi wata Turansufoma dake bayan ofishin da kuma wata da aka kafa a gaban ofishin, wanda hakan ya tada wuta.
Wani shaidan gani da ido, Abosede Oluwaseun, yace: “Jim ka?an bayan taron yau, mutane sun bar wurin, yan bindigan suka zo a motoci biyu, Bas da kuma Sienna, suka aje su a ?ayan gefen.” “Na cikin motocin suka fito suka nufi ginin ofishin ?auke da bindigu suka bu?e wuta.
Ba zan iya ?irga yawansu ba amma suna da yawa. Sun harbi Turansufoma dan kunna wuta cikin sa’a runfunan dake wurin suka kama da wuta.”
