Labarin dake shigo mana daga jihar Taraba na bayyana cewar Jolly Nyame, tsohon gwamnan jihar a cikin ranakun karshen mako ya samu kyakkyawar tarbar girma daga jama’a bayan ya dawo Taraba sakamakon rangwamen da ya samu.
A watan Afirilu, taron majalisar zartarwa ta kasa wacce ta samu jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi rangwame ga mazauna gidan yari 159 da suka hada da Nyame da Joshua Dariye tsohon gwamnan Filato.
Tsoffin gwamnonin wadanda aka garkame sakamakon cin amanar kasa da damfara, an yi musu rangwame saboda shekarunsu da kuma halin da lafiyarsu ke ciki.
An yankewa Nyame hukunci shekaru 14 a gidan maza a 2018 sakamakon waskar da kudaden al’umma da suka kai N1.64 biliyan, amma an rage masa zuwa shekaru 12 a gidan yari a 2020 bayan hukuncin kotun koli wanda ya tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara kan lamarin.
Hukuncin majalisar zartarwar ya janyo cece-kuce inda ‘yan Najeriya ke kwatanta hakan da koma baya wurin yaki da rashawa, amma fadar shugaban kasa ta kare kanta.
A watan Augusta, an sako Nyame daga gidan gyaran halin dake Kuje a babban birnin tarayya na Abuja. A cikin kwanakin karshen mako, tsohon gwamnan Taraba ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Danbaba Danfulani Suntai dake Jalingo a jihar Taraba inda ddubban jama’a suka dinga masa maraba.
