An Zo Wurin: An Fallasa Sunayen Masu Daukar Nauyin Ta’addanci A Najeriya

Mai ba Shugaban ?asa Shawara a kan Tsaro, Babagana Manguno ya baiyana sunayen ?ungiyoyin da su ke ?aukar nauyin ta’addanci a Nijeriya da sauran ?asashen Afirka.

Da ya ke jawabi a yayin bu?e taron horo karo na 14 ga gamaiyar ?ungiyoyin malamai, masu wa’azi da limamai na ?asashen Afirka da ke kan Sahara a Abuja, Manguno ya lissafo ?ungiyoyin da Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin, ?ungiyar Tallafawa Addinin Musulunci, JNIM da kuma ?ungiyar Musulmi ta ?asashen Sahara, ISGS.

Ya ce duk aiyukan ?an ta’addan da ke addabar Afirka tun shekarar 2016, ya na samun tallafi ne daga ?ungiyar Musulmi ta ?asashen Sahara, ISGS, wacce ta ke aiyukan ta a Mali, da kuma ?asashe irin su Nijer da kuma Burkina Faso.

“Sannan sai kuma su Nasr al-Islam Wal Muslimin, ?ungiyar Tallafawa Addinin Musulunci su ke ?ara ?arfafa aiyukan su, inda hakan ke ci gaba da haifar da razani na zaman lafiyar yankunan.

“A Nijeriya kuma, Boko Haram da ISWAP ne su ka mamaye aiyukan ?an ta’adda a Arewa-maso-Gabas na kasar nan,”

Manguno ya ?ara da cewa dole ne a hada kai a ya?i aiyukan ?an ta’adda, inda ya ce babu wata bindiga da ta fi wayar da kai da bada ilimi tun daga tushe karfi.

Related posts

Leave a Comment