Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta fitar da sanarwar da ke cewa shugaban na daukar matakan siyasa a ?ashin kansa, ba tare da katsalandan daga mutanen da ake tunanin suna juya gwamnati ta bayan fage ba da ake kira ‘Cabal’.
Sanarwar na dauke ne da sa hannun mataimaki na musamman ga shugaba kan yada labarai Malam Garba Shehu.
Wani bangare na sanarwar ya ce ”Shugaba Buhari na daukar matakansa ne kuma ya aiwatar da su ba tare da tsoma baki daga wasu wai su ‘cabal’ ko wasu masu uwa a bakin murhu ba.”
Sanarwar na zuwa ne bayan jita-jitar da ke yawo a kafafen yada labarai da ke cewa shugaban ne ya yi uwa da makarbiya wurin zaben fid da gwani da aka yi kwanakin baya, da ya samar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Haka kuma ta ce irin yadda aka gudanar da zabe fid da gwani na dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya nuna cewa Shugaba Buhari ba mai mulkin kama-karya ba ne.
