Matsalolin Najeriya Sun Gagari Kundila – Obasanjo

An bayyana halin ?a?a ni kayi da Najeriya ta shiga ciki musamman a bangaren tsaro a matsayin wani lamari da ya fi karfin mutum guda lamari ne wanda ya gagari Kundila.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Tsohon Shugaban kasa Obasanjo a yayin wata tattaunawa da aka yi dashi dangane makomar Najeriya nan gaba.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dage da yin addu’a da kai kukansu ga Allah domin magance matsalar tsaro da ta mamaye kasar nan a yanzu ta hana ta motsawa.

Obasanjo ya yi wannan magana ne a ranar Asabar a Abeokuta, jihar Ogun, yayin bikin karin kumallo karo na 16 wanda kungiyar kiristocin Najeriya (CAN), reshen jihar Ogun ta shirya don karrama shi.

Obasanjo ya ce kalubalen da ke gaban Najeriya ya wuce abin da ‘yan kasa da shugabannin za su iya dauka, amma ba su karfin Allah ba.

Ya nanata mahimmancin addu’o’i wajen magance matsalolin ya kara da cewa Najeriya na bukatar warkarwa daga Allah. “Halin da ake ciki a kasarmu na bukatar dukkaninmu da mu yi kuka ga Allah cikin addu’oi da roko,” in ji shi.

“Da alama mun cika da rashin sanin yadda za mu magance rikicin kasar mu. Amma babu abin da ya fi karfin Allah. Wannan shine dalilin da yasa muke nan. Muna da kalubale. Wadannan sun fi karfin abin da za mu iya dauka.

Dole ne mu yi kuka ga Allah don ya taimake mu. “Kasar mu na bukatar warkewa. An fi karfinmu, wadanda suke cikin gwamnati, masu zartarwa, ‘yan majalisa, ma’aikatan gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, abin ya wuce karfinmu.

Related posts

Leave a Comment