Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar bangaren su Malam Shekarau, tsohon gwamnan Kano ya za?i Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaban jamiyyar APC. Yayin da bangaren gwamnati ya za?i Abdullahi Abbas a matsayin shugaba.
Sun yi zaben ne a wani wuri a Janguza da ke yankin ?aramar hukumar Tofa.
Wannan na zuwa bayan ?angaren gwamna Ganduje ya za?i Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano.
Bayanai sun ce tuni shugabannin ?angarorin biyu suka yi jawabin amincewa da matsayin.
Hakan ya ?ara fito da ?araka tsakanin ?a?an APC a jihar Kano, yayin da jam’iyyar ke shirin tunkarar za?en 2023.
