Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta ?asa INEC ta tabbatar da kai hari kan ofishinta da ke ?aramar hukumar Oru ta yamma a jihar Imo da ke kudu maso gabashin ?asar.
A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce an kai harin ne da misalin ?arfe 4:00 na asubahin ranar Lahadi.
Hukumar ta ce harin ya shafin babban ?akin taro na ofishin tare da lalata kujeru da sauran kayyaki a ?akin taron.
A ‘yan kwanakin nan dai ana samun yawaitar hare-hare kan ofisoshin hukumar a ?ananan hukumomin jihar.
A ranar Asabar ma dai rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta ce dakarunta sun samu nasarar da?ile wani hari da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne tare da wata ?ungiya mai ?awance da ita da ake kira Eastern Security Network, da aka fi sani da ESN suka kai kan ofishin hukumar za?e na ?aramar hukumar Orlu da ke jihar.
Hukumar ta ce wannan shi ne hari na bakwai kan ofisoshinta a jihohi biyar cikin wata hu?u.
