Labarin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar ‘Yan bindiga sun kai hari tare da sace masallata kusan 20 a wani masallaci a ?auyen Maigamji da ke yankin ?aramar hukumar Funtua a jihar.
R?ahotonnin sun ce maharan sun kai farmaki masallacin ne ranar Asabar da daddare lokacin da masallatan suka taru domin gudanar da sallar Isha’i.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar katsina SP Gambo Isah ya shaida wa BBC cewa an raunata limamin masallacin tare da wani mutum guda, an kuma sallamo su daga asibiti bayan yi masu magani.
SP Gambo ya ce tawagar jami’an tsaro da ta ?unshi sojoji da ‘yan sanda da ‘yan sa kai sun samu nasarar ku?utar da wasu daga cikin wa?anda aka sacen.
To amma ya ce har yanzu ba a ga mutum 13 ba. Ya kuma ?ara da cewa jami’an tsaro na bakin ?o?arinsu wajen ganin sun ku?utar sauran mutanen da suka rage a hannun maharan.
Harin dai shi ne na baya-bayan nan, yayin da ?asar ke fama da yawaitar hare-haren masu garkuwa da mutane domin neman ku?in fansa.
Jihar Katsina – wadda ita ce mahaifar shugaban ?asar Muhammadu Buhari – na cikin jihohin ?asar da ke fama da tashe-tashen hankula masu ala?a da ayyukan ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.
Matsalar rashin tsaro dai ta kasance wani babban al’amari da jam’iyyun siyasa a ?asar ke sanyawa cikin manyan manufofin ya?in neman za?ensu, yayin da ?asar ke tunkarar babban za?e a farkon shekara mai kamawa.
