Buhari Ya Dora Tubalin Ginin Sabuwar Hedikwatar ECOWAS A Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ?addamar da tubalin ginin sabuwar hedikwatar ?ungiyar Raya Tattalin Arzi?in ?asashen Afirka ta Yamma, Ecowas a Abuja babban birnin tarayya.

Shugabannin ?asashen Guinea Bissau Umaro Embaló, da na Saliyo Julius Maada Bio, da Shugaban Ecowas Omar Alieu Touray, da Jakadan China a Najeriya Cui Jianchun, su ne suka taya Buhari saka ?ambar ginin a ranar Lahadi.

Ana sa ran kammala sabuwar hedikwatsar a shekara ta 2025.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana cewa hamsha?in ginin, wanda gwamnatin China ta samar da ku?in ginawa, zai ?arfafa zumunci a tsakanin ?asashen Afirka.

Ginin zai kuma wakilci al’ummar Afirka ta Yamma mutum miliyan 380 sannan zai kasance matsuguni ga manyan cibiyoyin Ecowas uku, ciki har da ginin hukumar gudanarwar ?ungiyar da Kotun Ecowas, har ma da Majalisar Dokokin Ecowas.

A gefe guda kuma, shugabanin mambobin ?ungiyar na gudanar da taro karo na 62.

Related posts

Leave a Comment