Babban basaraken kasar yarbawa, Oba Abdulrasheed Akanbi, Oluwa na Iwo, ya rubuta wasika ga Shugaba Muhammadu Buhari don nema wa Sunday Igboho afuwa.
Basaraken na Yarbawa ya ce Sunday Igboho dansu ne amma akwai kuruciya da kuskure cikin hanyar da ya ke gudanar da gwaggwarmayarsa Oba Abdulrasheed Akanbi ya ce Igboho ya sha wahala sannan ya gane kurensa kuma ya yi alkawarin zai mika shi ga idan har an masa afuwa.
Oba Abdulrasheed Akanbi, ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Igboho afuwa, Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an hukumar yan sandan DSS sun kai samame a gidansa da ke Ibadan a makon da ta gabata inda aka kashe mutum biyu. Ka yiwa Igboho afuwa, zan kawo shi tattauwar zaman lafiya, Sarkin Yarbawa ya roki Buhari.
DSS ta yi holen mutanen da ta kama a gidansa da makamai da wasu kayayyaki da aka samu, Igboho ya samu ya tsere a yayin da mutanensa ke musayar wuta da jamian DSS yayin samamen. Nan take aka ayyana nemansa ruwa a jallo aka shawarci ya mika kansa domin babu inda zai boye.
A martaninsa, Oluwo, cikin wasikar da ya rubuta game da lamarin Igboho ya shawarci Shugaban Kasa ya sassauta farautar da ya ke yi wa Igboho.
Wani sashi na wasikar ya ce: “Sunday Igboho ya yi fice ne a matsayin dan gwagwarmaya da ke son kwato hakkin wadanda ake zalunta. Ban san tsarinsa ba saboda ba tare muke aiki ba. Duk lokacin da na samu bayani game da abin da ya ke yi, na kan kira shi in bashi shawara. Igboho ya kasa gane banbanci tsakanin gwagwarmaya ta gwamnati da gwagwarmaya tsakanin kungiyoyi. A wani lokacin ya zagi masu ruwa da tsaki. Ina cikin mutanen farko da suke kira ga Nigeria daya.
A matsayina na mahaifi, na yafe masa. Ina rokonka a matsayin shugaban Nigeria ka yafe wa danmu Chief Adeyemo Sunday Igboho. “Dan koyo ne a harkar gwamnati. Ya yi alkawarin zai saurare mu. Ina rokon mai girma shugaban kasa ya sasauta farautar da ya ke yi wa Igboho. Ina fatan wannan rubutun zai karfafa zaman hadin kan Nigeria. Ina yi wa mai girma shugaban kasa alkawari daga yanzu Igboho zai fara takatsantsan. Ya sha wahala sosai. Zai sasauta fafutikarsa. Zan kawo shi domin tattaunawar zaman lafiya a lokacin da ya dace.”
