Zamfara: Sabon Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Mutane 42

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar akalla mutum arba’in da biyu tsagerun yan bindiga suka hallaka yayinda suka kai hari kauyuka biyar a karamar hukumar Maradun dake jihar da daren Alhamis.

Garuruwan da aka kai hari sun hada da Tsauni, Gidan-Baushi, Gidan-Adamu, Wari da Gidan-Maidawa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wani dan garin, Malam Buba Faru, ya ce yan bindiga sun dira garin kan babura sama da 100. Buba yace dirarsu ke da wuya, suka fara harbin mutane suna kona gidaje da runbunan abinci.

“Suna harbin kan mai uwa da wabi yayinda suka shiga garuruwan. Sun kai wa manoman dake gonakinsu hari.

“Zuwa yanzu dai jami’an tsaro da yan sa kai sun gano gawawwaki 42 Buba ya kara da cewa tuni akayi jana’izar mamatan ranar Juma’a.

Sai dai anashi ?angaren Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya ce mutum 35 kadai aka kashe a tattaunawarsa da manema A cewarsa, an tafi da gawawwakinsu garun Faru inda za’a biznesu.

Kakakin yan sandan yace: “Jami’an hukumar basu samu damar shiga garuruwan lokacin da ake kai harin ba saboda rashin kyan hanya.” Ya kara da cewa yan sanda na kokari matuka don damke yan bindigan.

Related posts

Leave a Comment