Babu Gaskiya A Labarin Cewa Zan Koma APC – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ?aryata labaran da ake ta yadawa wai zai canja sheka daga PDP ya koma APC ranar 12 ga Yuni.

Matawalle ya ce bai fa?i haka kuma ma hakan baya cikin lissafin sa a yanzu.

Game da korar kwamishinoni da yayi ya ce babu abinda ya ha?a hakan da wani shiri wai nasa na komawa wata jam’iyya.

” Na shekara biyu kenan a kan mulki, saura shekara biyu wa’adin zango na na ?aya ya cika, saboda haka sai naga ya kamata in yi irin wannan tanka?e da rairaya, wato in yi garambawul domin kuma mu tsara yadda za mu tunkari shekaru biyun da suka rage mana masu zuwa.

Da aka tambaye shi ko akwai wata tattaunawa da yake yi da wasu kan yiwuwar canja sheka, ya ce ” Tattaunawa a wurin ?an siyasa ai ya zama dole, tattaunawa kamar da ?an siyasa, abokan ka, mutane da talakawan ka duk dole ka ri?a tattaunawa da su, ni irin wannan tattaunawa na ke yi.

Related posts

Leave a Comment