Dan Takarar Gwamna Tsohon Babban Hafsan Sojin Sama Ya Ziyarci Bauchi

Daga Adamu Shehu Bauchi

Dan’takarar Gwamnan jihar Bauchi, tsohon babban hafsan Sojin sama kuma Jakadan Najeriya a kasar Chadi, Mashal Abubakar Sadiqque ya ziyarci jiharsa ta haihuwa dan’gane da hidimar zaben gama gari dake karatowa a shekarar dubu biyu da ashirin da uku 2023.

Jigajigan Yan’siyasar jihar daga bangarori dabam-dabam ne suka tarbe shi a filin tashi da saukan jirage na kasa dake Jihar, musamman yayan Jam’iyyar APC Wanda a karkashin Jam’iyyar ne yake zawarcin kujerar Gwamnan jihar.

Jimkadan bayan ya isa gida domin ganawa da magoya bayansa, kana Kuma muryar yanci ta samu zan’tawa da masu ruwa da tsaki a tafiyar takarar Saddique Abubakar, tsohon Kwamishinan harkokin Addinai Alhaji Salisu Baurau a gwamnatin baya a Jihar.

Yace wan nan tafiyar neman Gwamnan Abubukar za suyi da gaske ne saboda suna bukatar chanza Gwamnati mai chi a halinyanzu a Jihar domin kawo ci gaba mai ma’ana da kuma farfado da tattalin arzikin jihar.

Ya kara da cewa, “Dan takarar gwamnan Sadiqque Abubakar jajirtacce ne kuma yana da himma ta wajen aiki ma al’umma tun yana kan kujerar babban hafsan Sojojin saman Najeriya, acwarsa ya chanchanchi ya zama Gwamnan jihar Bauchi”

Shima wani jigo a siyasar Bauchi tsohon dan’majalisar tarayya Alhaji Isa Yakubu Toro ya yaba da irin gogewarsa akan aiki tukuru, “Yayi aiki mun gani a Najeriya baki daya duk wanda yayi irin abunda yayi a kasa baki daya, in ya samu dama zai yi ma Jihar sa ta haihuwa abun da yafi haka saboda yana da kishin kasar sa sosai”.

Daga karshe dan’takarar Sadiqque Abubakar kuma mai neman Jam’iyyar sa ta APC ta bashi daman ya daga Mata tuta a matsayin dan takar kujerar gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2023.

Yayi ma magoya bayansa godiya da irin karamcin da suka nuna masa ziyararsa Karin Farko a mtsayin Mai nema atsayar dashi takara Gwamnan Jihar Bauchi

Related posts

Leave a Comment