Adamawa: Ina Burin Sake Dawowa Gwamna – Bindow

Rahotanni daga Yola babban birnin jihar Adamawa na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Umar Jibrilla Bindow, ya bayyana burinsa na neman wani wa’adi a matsayin gwamna a karkashin APC a 2023.

An ruwaito Umar Jibrilla Bindow yana cewa zai so a ba shi wata damar domin ya karasa ragowar shekaru hudu da suka rage masa a gidan gwamnati.

Da yake zantawa da manema labarai a garin Yola, jihar Adamawa a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu 2022, Jibrilla Bindow ya nemi goyon bayan al’ummar Jihar da su sake bashi damar.

Bindow ya roki sauran masu neman kujerar gwamna a Adamawa a karkashin APC su kyale shi ya koma kan mulki domin ya kammala ayyukan da ya fara.

A cewar tsohon Sanatan, idan har ya sake zama gwamna, mutanen Adamawa za su ga cigaba a jihar. “Na yi abubuwa da-dama a lokacin da na ke gwamna, kuma ina da buri da yawa da na ke da shi ga jihar nan idan har aka yi dace aka sake zabe na 2023.”

Sanata Umar Jibrilla Bindow wanda ya yi mulki tsakanin 2015 da 2019 ya sha kashi ne a hannun Ahmadu Umaru Fintiri na Jam’iyyar PDP a lokacin da ya nemi ya zarce a mulki.

Related posts

Leave a Comment