Biyo bayan wani hari da aka kai a ofishin yan sanda dake Ngurore dake jahar Adamawa rundunan yansandan jahar ta kara tura Jami anta don maido da zaman lafiya a cikin garin na Ngurore.
Kwamiahinan yan sandan jahar CP Muhammed Ahmed Barde ne ya baiyana haka a wata sanarwa dauke da sanya hanun kakakin rundunan D S P Suleiman Yahaya Nguroje wanda aka rabawa manema labarai a yola.
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne dai suka kai hari a ofishin yan sanda dake Ngurore da gidan wani mai suna Alhaji Umaru duk a cikin garin na Ngurore.
Hakan yasa kwamiahinan yan sandan jahar Adamawa ya bada umurnin tura Jami an yan sandan ciki harda yan sandan kwantar da tarzoma domin ganin an dakile aiyukan yan ta addan a fafidin jahar baki daya.
Kwamiahinan yan sandan wato CP Muhammed Ahmed Barde ya tabatarwa al ummar jahar cewa rundunan a ahirye take ta kare rayukan jama a dama dukiyoyinsu don haka nema ya kirayin jama a musammanma wadanda ke cikin garin na Ngurore da sucigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.
Acewar kwamishinan dai zai aiki kafada da kafada da dukkanin masu ruwa da tsaki domin ganin an dakile aiyukan yan ta adda a fadin jahar ta Adamawa baki daya.
Don hake nema yake shawartar al ummar jahar da sucigaba da baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin sun cimma burinsu na wanzar da zaman lafiya a fadin jahar baki daya.
