Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gaggawar da ?asashen Malaysia da Taiwan su ka yi na kwashe dukkanin ‘Indomie Special Chicken’ daga kantina da kasuwannin ?asashen biyu, ya ka?a hantar Najeriya da sauran ?asashen duniya.
?asashen biyu sun dakatar da sayarwa da cin nau’in Indomie ?in biyo bayan gano sinadarin ‘ETHYLENE OXIDE’ mai haddasa cutar kansa a cikin Indomi ?in.
Cibiyoyin kula da lafiyar abinci da magunguna ta ?asashen biyu su ka gano sinadarin bayan wani binciken ?wa?waf da su ka gudanar.
Tuni ita ma Najeriya ta zabura, yayin da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ?asa (NAFDAC) za ta fara binciken samfuran Indomi ?in da ake ci da sayarwa a Najeriya.
NAFDAC ta tabbatar wa PREMIUM TIMES haka a ranar Lahadin nan da safe cewa za ta fara gudanar da binciken domin ganowa da tabbatar da gaskiyar abin da ?asashen Taiwan da Malaysia su ka ce sun gano.
Sinadarin Da Taiwan Da Malaysia Su Ka Gano A Cikin Indomi:
Ma’aikatar Lafiya a Taipei, babban birnin ?asar Taiwan ta ce ta gano sinadarin ,’ethylene oxide’ mai haddasa cutar kansa a nau’ukan Indomi biyu, wato Indomie Chicken flavour, a wani gwajin ingancin abincin da su ka yi.
Ta ce sun gano cewa samun sinadarin mai haddasa kansa a jikin mutane da aka yi a cikin Indomie, ya nuna an kauce wa ?a’ida da sharu??an ingancin abinci kafin a kai shi kasuwa.
Sinadarin Da Malaysia Ta Gano A Cikin Indomi:
Ma’aikatar Lafiya ta Malaysia ta ce ta yi gwaji a samfura 36 na indomi, tun daga 2022, kuma ta gano cewa tabbas akwai sinadarin ‘etheylene oxide’ mai haddasa kansa a jikin ?an Adam a cikin su.
Sai dai kuma kamfanin Indofoods na ?asar Indonesia masu yin Indomie sun ?aryata zargin cewa su na amfani ko akwai sinadarin da ke haddasa kansa a cikin nau’ukan abincin na su.
Sai dai tuni Taiwan da Malaysia sun bada umarnin a janye Indomie daga kantina da kasuwannin ?asashen biyu.
A Najeriya, Darakta Janar ta NAFDAC, Mojisola Adeyeye, a safiyar ranar Lahadi ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa daga ranar Talata mai zuwa za su bazama yin gwaji, wato daga ranar 2 Ga Mayu.
Ta ce tuni jami’an gwaji a hukumar sun shirya tsaf, ta yadda da zarar sun kammala, sannan hukumar za ta yi wa jama’a bayanin abin da ta gano.
