Muna Kiran Kasashen Duniya Su Kakaba Wa Buhari Takunkumi – PDP


Jam’iyyar PDP ta yi kiran gaggawa ga ?asashen duniya cewa su haramta wa Shugaba Muhammadu Buhari shiga cikin duniya bayan ya kammala wa’adin sa na shekaru takwas a ranar 29 Ga Mayu.

Wannan kira ya zo ne a matsayin raddi ga bayanin da Buhari ya yi cewa “ci-da-zuci da hangen Dala ne su ka kayar da jam’iyyun siyasa a za?en shugaban ?asa na 2023.

Buhari ya yi bayanin a lokacin da ?ungiyar Gwamnonin Arewa su ka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a Fadar Shugaban ?asa.

Yayin da ya ke yi masu jawabin maraba ne ya bayyana abin da ya ce ya kayar da ‘yan adawa a za?en shugaban ?asa na 2023.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jam’iyyun adawa sun fa?i za?en 2023 ne saboda ci-da-zuci da hangen-Dala, ba shiga birni ba.

Buhari ya ce wannan ci da zucin jam’iyyu ya bai wa APC ?arfin samun sake yin nasarar kafa mulki ko kuma nasarar za?en 2023.

Buhari ya yi wannan fashin ba?in ne a lokacin da ya kar?i ziyarar Gwamnonin APC, bisa jagorancin Gwamna Atiku Bagudu wanda shi ne Shugaban ?ungiyar Gwamnonin APC.

“Jam”iyyun adawa sun ?ata lokaci su na ta kiran masu goya masu baya daga ?asashen waje cewa za su kayar da APC. Amma sai jam’iyyar mu ta yi masu kwasar-karan-mahaukaciya, ta zubar da su ?asa.

“To yanzu ci-da-zucin su ya kai su ya baro su, maimakon nasara, sai matsalolin su ke ta ?aruwa. Sun kasa bayyana wa masu goyon bayan su daga waje, gamsassun dalilan da ya sa su ka kasa kayar da mu za?e.”

Buhari ya shawarci gwamnonin APC su ?ara ha?a kai domin magance dukkan ?alubalen da ke gaban su.

Buhari ya yi dogon bayani dangane da rayuwar sa bayan ya yi ritaya, ya ce zai shafe watanni shida a Daura, daga nan ya koma Kaduna baki ?aya.

Buhari ya gode wa Gwamna Nasiru El-Rufai saboda ayyukan raya jihar da ya samar a Kaduna.

Ya ce gyaran da Buhari ya yi wa Kaduna zai sau?a?a masa yin rayuwa a cikin sau?i idan ya tare a Kaduna, bayan ya yi watanni shida a Daura.

Bagudu ya ce sun je ne domin su yi wa Buhari Barka da Sallah kuma su yi masa fatan alheri.

Da ya ke wannan ce siyasar su ta farko tun bayan kammala za?e, gwamnonin sun taya Buhari murnar sake lashe za?e da APC ta yi.

Raddin PDP Ga Buhari:

A cikin raddin da Sakataren Ya?a Labarai na PDP, Debo Ologbondiyan ya fitar a ranar Lahadi, ya ce ya kamata duniya ta sani cewa PDP ba ta fa?i za?e ba, amma dai kayar da ita aka yi. Don haka ne ma ta garzaya kotu, domin ta baje hujjojin ta.

PDP ta yi kira ?asashen duniya su hana Buhari shiga cikin su, saboda ya karya al?awarin kare dimokra?iyya, wanda ya yi a ranar 17 Ga Fabrairu, 2022 a Brussels, babban birnin ?asar Belgium.

Debo ya ce bugun ?irjin da Buhari ke yi a yanzu kan nasarar da APC ta yi a za?en da duniya ta tabbatar cewa ha sahihi ba ne, ya nuna cewa da sanin sa aka samu duk wani cikas ?in da aka samu a lokacin za?en kenan.

Related posts

Leave a Comment