An Dawo Da Dala Miliyan 700 Da Barayin Gwamnati Suka Jibge A Waje – Malami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya ce gwamnatin tarayya ta samo sama da dala miliyan 700 a cikin shekaru hudu na daga cikin kudaden da barayin gwamnati suka wawure suka jibge a ?asashen ?etare.

Malami Ya sanar da hakan ne a ranar Talata a wani taron da aka yi kan shige da ficen kudi ba bisa ka’ida ba da kuma samo su wanda hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta shirya.

Ya ?ara da cewar kasashen da ke tasowa a Afrika suna rasa sama da $148 biliyan ga rashawa a kowacce shekara wanda hakan ke taimaka wajen mayar da hannun agogo baya.

“Najeriya ta hanyoyin da take bi da kuma hadin kan wasu kasashe, ta samu an dawo da sama da dala miliyan 700 daga Amurka, Ingila, Bailiwick ta Jersey, Switzerland da Ireland a cikin shekaru hudu da suka gabata,” yace.

“Har a halin yanzu muna aiki da wasu kasashen ketare domin tabbatar da cewa an dawo da dukkan kadarorin Najeriya dake can.”

Malami wanda ya samu wakilcin Juliet Ibekaku-Nwagwu, babban mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin shari’a, ta jajanta yadda manyan kudade ke fita daga Afrika ba bisa ka’ida ba wanda hakan yasa rashin tsaro ke cigaba da tsananta sannan ake rasa cigaba.

“Babu shakka, wannan fitar kudin ke kawo rashin cibiyoyin lafiya da ilimi, talauci da rashin ababen more rayuwa a kasashen Afrika,” ya kara da cewa.

Related posts

Leave a Comment