Sulhu: El Rufa’i Zai Gana Da Shugabannin Kwadago Yau A Abuja

Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, da shugabannin kungiyar kwadago NLC zuwa wajen taron gaggawa data shirya domin yin sulhu a tsakanin su, da niyyar kawo karshen rikicin dake tsakanin bangarorin biyu.

Gwamnatin ta sanya ranar yau Alhamis 20 ga watan Mayu domin tattaunawar sulhu tsakanin ?angarorin biyu a babban Birnin tarayya Abuja.

Wannan na cikin ?o?arin da gwamnatin tarayya ke yi domin dakatar da yajin aikin da kungiyar ke yi gaba ?aya da kuma rikicin dake tsakanin gwamnatin Kaduna da ?ungiyar ?wadagon kan sallamar ma’aikata a jihar Kaduna.

Gwamnatin ta gayyaci ?angarorin biyu ne ta ofishin ministan kwadugo, Chris Ngige, domin ta shiga tsakani. An shirya yin zaman sulhun ne da misalin ?arfe 11:00 na safe a ofishin ministan Kwadago na ?asa ranar yau Alhamis a Abuja.

Wa?anda aka gayyata zuwa wajen taron sulhun sun ha?a da; Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i tare da manyan jami’an gwamnatinsa, da kuma shugaban kungiyar kwadago NLC, Ayuba Waba, tare da manyan shugabannin ?ungiyar.

Related posts

Leave a Comment