An Ceto ‘Yan Sandan Da ‘Yan Bindiga Suka Sace

Rundunar ‘yan sanda ta sanar da cewa an kubutar da manyan ‘yan sanda tara, dukkaninsu masu mu?amin ASP, da ‘Yan Bindiga suka sace tun ranar takwas ga watan Nuwamba na wannan shekarar a tsakanin jihar Katsina da Zamfara.

An sace manyan ‘yan sandan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, domin aiwatar da wasu muhimman ayyuka na musamman.

A cikin wani jawabi da kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba, ya fitar ranar Juma’a, ya ce wani binciken karkashin kasa da suka gudanar, bayan samun labarin sace jami’an, ya gano wurin da aka garkamesu.

An sace jami’an a tsakanin garin Kankara zuwa Sheme a jihar Katsina sakamakon mummunan harin da wasu ‘yan bindiga sanye da kayan soja suka kai a kan motar haya da suke ciki tare da wasu fararen hula.

“Basa dauke da makamai, kuma basa sanye da kakin aikin dan sanda a lokacin da aka kai musu harin cikin tsakar dare.

“Wasu ‘yan ta’adda, dauke da manyan bindigogi da ake zargin ‘yan bindiga ne, kuma sanye cikin kakin sojoji, su ne suka sacesu bayan sun kai wa motarsu farmaki yayin da suke tafiya cikin tsakar dare.

“Dukkaninsu masu mukamin ASP ne kuma suna kan hayarsu ta zuwa Gusau, jihar Zamfara, daga Maiduguri, jihar Borno a lokacin da tsautsayin ya faru,” a cewarsa.

Mba ya ce biyu daga cikin jami’an yanzu haka suna asibiti ana duba lafiyarsu, yayin da sauran bakwai suna samun kulawa ta musamman.

Related posts

Leave a Comment