Kaduna: El Rufa’i Ya Dakatar Da Wazirin Zazzau

Gwamnatin jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ta dakatar da Shugaban kwamitin masu zaben sarkin Zazzau, Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu har sai abin da hali ya yi.

Hakazalika Gwamnatin ta gargadi Iyan Zazzau Bashar Aminu da sauran mambobin kwamitin zaben sarkin uku su canza lauyansu zuwa lauyan gwamnati a karar da suka shigar kotu, kan nadin Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Idan jama’a basu mance ba Iyan ZazzauBashar Aminu, ya shigar da kara kotu inda ya ke kalubalantar nadin Ahmad Bamalli a matsayin sabon sarkin masarautar Zazzau.

Gwamnatin jihar Kaduna, a wasikar da sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin kananan hukumomi ya sanya wa hannu a madadin kwamishanan, ta sanar da dakatar da Wazirin Zazzau.

Bincike ya nuna cewa sabon Sarkin da Gwamnatin jihar sun yiwa masu zaben sarki barazanar su canza lauyansu zuwa lauyan jihar, saboda su sanya hannu kan jawabin rantsuwa.

Barazanar da Sarki da gwamnatin jihar keyi ne ya sa aka aika wasikar tuhumar ranar 12 ga Nuwamba, 2020.
Kawo yanzu dai, daya daga cikin masu zaben sarkin ya amince da canza lauyansa zuwa na gwamnati.”

A baya can mun kawo muku rahoton cewa an aikewa ‘yan majalisar sarki takardar tuhuma mai taken “rashin halartar taron tattaunawa da ma’aikatar kananan hukumomi ta shirya”

Daga cikin wandanda aka aikewa takardar akwai limamin Zazzau, Wazirin Zazzau, Limamin Kona da Makama Karami kan rashin halartar wani taro da aka yi kan shirin bikin mika sandar sarauta ga sabon sarkin Zazzau.

An bada awa 48 ga wanda suka karbi tuhumar da suyi bayani, sai dai wani rahoto ya nuna wasu daga cikin masu zaben sarkin, basa jin dadin yadda al’amura ke gudana a masarautar mai da?a??en Tarihi.

Related posts

Leave a Comment