Makomar Najeriya Na Hannun Arewa Ta Tsakiya – Saraki

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya ce yankin arewa ta tsakiya ce zuciyar Najeriya kuma yankin zai iya ciyar da kasar nan gaba.

A cewar Saraki, yankin ne zai kawo mafita ga Najeriya nan gaba, kamar yadda yace, arewa ta tsakiyar tana da ma’adanai masu tarin yawa, wanda hakan zai kawo kudi Najeriya.

Saraki ya bayyana hakan ne lokacin da tawagar shugabannin kungiyar jama’ar arewa ta tsakiya (NCPF) su ka kai masa ziyara gidansa da ke birnin tarayya Abuja makon da ya gabata.

A cewarsa, Arewa ta tsakiya mallakin Najeriya ce, kuma wajibi ne a dubi yankin idan 2023 tayi, domin samar wa kasar makoma ta ?warai.

An zabi tsohon shugaban majalisar dattawa a matsayin jigon NCPF, kuma ya nuna farin cikinsa na wannan matsayi da aka bashi. A cewarsa, babban dalilin kirkirar NCPF shine samar da hadin kan ‘yan arewa gaba dayansu, sannan da neman shawarwarin juna idan wani al’amari ya bullo.

Related posts

Leave a Comment