Ganduje Ya Hanani Kudin Fansho Tsawon Shekaru 6 – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Ganduje na take masa hakkinsa, na hanashi fansho tsawon shekaru 6 tun bayan da ya bar karagar mulki.

Kwankwaso ya yi korafin cewa shekara shida kenan Ganduje ya ki biyansa kudin fansho, ya ki gina masa gida kamar yadda dokar jihar ta tanada. Hakazalika gwamna Ganduje bai gina masa ofishin da doka ta bukaceshi ba.

Kwankwaso ya ce an yi hakan ne da gangan saboda ya koma jam’iyyar hamayya. Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da BBC Hausa.

“Da ace ina tare da su, da sun biya ni kudaden fansho na a kowanne wata. Na yarda hakan na faruwa ne saboda ina bangaren adawa. Saboda haka su je su rike.”

Related posts

Leave a Comment