Akwai Kauyawan Dake Taimakon ‘Yan Bindiga Da Bayanai – Sanata

Rahotanni daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewa Sanata Sani Musa, mai wakiltar gabashin jihar Neja inda ‘yan bindiga suke cin karen su babu babbaka, ya yi kira ga mazauna kauyuka da matasa da su hada kawuna don ganin an zakulo gami da kawar da ‘yan bindiga a jihar.

Ya kara da kira ga jami’an tsaro da su yi amfani da dabarbarun zamani wajen ganin sun yi gaba da gaba da ‘yan ta’addan kamar yadda ya roki gwamnatin tarayya da ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ake yawan kai harie hare.

Sanatan ya bayyana hakan ne ayayin wata tattaunawar da ya yi da manema labarai, ya sanar da yadda wasu al’amura marasa dadi suke faruwa a jihar, inda suke nuna yadda wasu ‘yan kauye suke da hannu dumu-dumu a ta’addanci, har wasu suke zama ‘yan leken asirin ‘yan bindigan wanda hakan ke matukar wahalar da jami’an tsaro.

Musa ya ce wannan ba lokacin siyasa ba ne, bayan tashin hankalin da ake ciki, lokaci ne da duk masu rike da mukamai za su hadu guri daya domin yakar bayyanannun makiyan al’umma.

“Wani lamari da ya faru kwanan nan ya bayyana yadda wasu mazauna kauye suka zama ‘yan leken asiri ga ‘yan bindiga, wanda hakan ke share musu hanyar kawo hari yankunan,” a cewar Sanata.

“Ina rokon matasa musamman a yankunan da al’amarin ya shafa da su zakulo masu taimaka wa ‘yan ta’adda kuma su kai karar su inda ya dace don a dauki mataki.

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki matakin da ya dace don ganin ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ta’addancin ya shafa, yayin da sojojin za su yi amfani da dabarbarun zamani wajen yin fito na fito da yakar hatsabiban”.

Related posts

Leave a Comment