Hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa INEC, ta fitar da jerin sunayen ?an takarar shugaban ?asa da majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilai na dukkan jam’iyyun ?asar da za su fafata a za?ukan 2023.
INEC ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talata, 20 ga watan Satumban 2022, inda ta ce jerin na ?u she ne da sunayen ?an takara daga jam’iyyu 18.
An wallafa jerin sunayen na ?an takara daga dukkan maza?un ?asar a shafin intanet na INEC.
Za a gudanar da za?en shugaban ?asa da na majalisun dokokin tarayya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 sai na gwamnonin da majalisun dokokin jihohi ranar 11 ga watan Maris din 2023.
A jerin sunayen, akwai ?an takarar shugaban ?asa da mataimakansu 18 daga jam’iyyu daban-daban, sai kuma ?an takarar majalisun tarayya daga jihohi 36 da babban birnin ?asar Abuja, ?ar?ashin jam’iyyu daban-daban.
Baya ga sunayen ?an takarar da ta wallafa, INEC ta kuma bayyana jinsi da shekaru da matakin ilimi na kowane ?an takara.
