Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Ziyarar Da Ya Kai Waje

Rahotannin dake shigo mana na bayyana cewa jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya isa Legas daga kasar Birtaniya a ranar jiya Lahadi.

An ruwaito cewa kafafen sada zumunta sun cika da jita-jitar cewa Tinubu ya ziyarci Ingila ne domin duba lafiyar shi amma ofishin sa na yada labarai ya karyata rahotannin, yana mai cewa tsohon gwamnan ya kai ziyarar aiki ne kawai.

Babban jigon siyasan ya isa Legas cikin koshin lafiya, ya kuma samu kyakkyawar tarba daga ?imbin jama’a masoya.

Related posts

Leave a Comment