A tattaunawar da gidan Rediyon BBC Hausa ya yi da ita jarumar Finafinan Hausa Aisha Najamu wadda aka fi sani da suna Nafisa Izzar So, ta bayyana cewar ko ka?an ba ta fatan aure a masana’antar Finafinan Hausa.
Aisha Najamu ta fadi hakan ne lokacin da take bayar da amsa ga tambayar da aka yi mata cewar ko tana da Saurayi a Kannywood sannan zata iya auren abokin sana’arta ta Hausa Fim?.
Ta bayyana cewar tana mutunta abokanan sana’arta na Hausa fim amma batun soyayya ko burin auren wani a ciki ba ta da wannan buri, inda ta yi rokon a manta da wannan tambaya kar a sake maimaitawa.
A’isha Izzar So wadda tace ita ‘yar asalin Jihar Jigawa ce, ta bayyana cewar ta ta?a aure kuma tana da yara, sannan har yanzu tana da burin sake yin aure amma ba a cikin masana’antar Kannywood ba.
Tauraron Jarumar ya fara haskawa ne a ‘yan shekarun nan musanman a cikin wani shirin Fim mai dogon zango mai suna “Izzar So” da ake da ake sanyawa a manhajar YouTube.
