Adamawa: ‘Yan Jarida Sun Koka Akan Halin Tasku Da Jama’a Ke Ciki

Kungiyar yan jaridu a Najeriya N U J shiyar jahar Adamawa ta koka dangane da tsadar rayuwa da al umma ke ciki na tsadar kayaki abinci dama sauran kayakin masarufi.

Kungiyar ta baiyana haka ne a wata takardan bayan taro da ta fitar bayan taron da ta gudanar a cibiyar yan jaridu take yola, fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Taron ya gudanae karkashin jagorancin shugaban kungiyar Ishaka Donald Dedan inda suka kirayi gwamnatocin a dukkanin matakai da suyi dukkanin abin da suka dace domin kawo saukin kayakin abinci domin ragewa al umma wahala da suke ciki.

Kungiyar ta yabawa gwamnatin Ahmadu Fintri dana tarayya bisa na mijin kokari da sukeyi na daukan matakain tsaro domin kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasar baki daya.

Sun kuma kirayi gwamnatocin da su kara kaimi wajen daukan matakan tsaro domin ganin an kawo karshen matsalar dake ciwa gwamnatin kasar tuwo a kwarya.

Kungiyar tace zata sanya ido domin tantance yan jaridu bogi a cikin membobinta, tare da kiran membobin kungiyar da su kasance masu gudanar da aiyukansu bil hakki da gaskiya domin samun cigaban kungiyar a jahar dama kasa baki daya.

Harwayau kungiyar ta kirayi yan Najeriya ta su cigaba da yin adu o i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo dukkanin matsalar tsaro a fadin kasar baki daya.

Related posts

Leave a Comment