Aisha Yesufu Ta Shiga Cikin Jerin Mata 100 Masu Daraja A Duniya

?ar gwagwarmayar Najeriya kuma shugabar ?ungiyar kiran #Bring back our girls; ta gwagarmayar ‘yammatan Chibok da aka sace, Aisha Yesufu, ta shiga jadawalin shaharrarrun mata masu fa?a aji 100 na duniya na shekarar 2020.

Sunan fitacciyar ?ar gwagwarmayar yazo a jere da na Sanna Marin wacce ta jagoranci ha?akar gwamnatin mata zalla, Michelle Yeoh; tauraruwar sabuwar halittar Marvel, da Sarah Gilbert; wacce ta jagoranci binciken allurar rigakafin Korona a jami’ar Oxford, tare da Jane Fonda; ?ar gwagwarmayar sauyin yanayi kuma jaruma.

Aisha Yesufu haifaffiyar jihar Kano ce, an haifeta 12 ga watan Disamba na shekarar 1974, Cikakkiyar Bakanuwa ce ‘yar birnin Kano.

Aisha Yesufu ‘yar gwagwarmayar zamantakewa da siyasa, kuma jagora a ?ungiyar #Bring back our girls, ?ungiyar da ta jawo hankalin duniya kan sace yara mata ?anana sama da 200 a wata makarantar Sakandiren ‘yammaata a Chibok, jihar Borno, a ranar 14 ga watan Afrilu, 2014, wanda ?ungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka sace su.

Aisha Yesufu ta na kan gaba a tafiyar kawo ?arshen rundunar SARS#EndSARS, wani kira da ya jawo hankalin duniya kan ta?argazar da sashe na musamman mai ya?i da fashi da makami(SARS) na rundunar ?an sanda ke aikatawa.

Iyayen Aisha dai ?an asalin jihar Edo ne, amma ita tashinta da girmanta duk a Kano ne,ta sha bayyana irin wahalhalu da ?alubalen da ta fuskanta saboda kasancewarta ita ka?ai ce ?iya mace wadda ta taso cikin maza.

A kwanakin baya ne dai aka ruwaito cewa ‘yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta yi shagube yayin mayar da martani ga Musulman da suka dinga caccakarta saboda ‘ta yi uwa, ta yi makarbiya’ a zanga-zangar ENDSARS.
Aisha, wacce sunanta ya kara karada gari saboda zanga-zangar ENDSARS, ta ce ko kadan hakan bai taba damunta ba.

Related posts

Leave a Comment