Adamawa: NDLEA Ta Sha Alwashin Magance Matsalar Shaye-Shaye

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa N D L E A shiyar jahar Adamawa ta laahi takwabin domin magance matsalar shaye shaye a fadin jahar ta Adamawa baki daya.

Kwamandan rundunan hukumar a jahar Adamawa Idris Muhammed Bello ne ya baiyana haka a lokacin da ya karbar tabar wiwi dama sauran miyagun kwayoyi wadanda yan sandan suka kama a shelkwatan rundunan yan sandan dake yola.

Idris Muhammed Bello yace hukumar ta N D L E A zata hada kai da rundunan yan sandan wajen yaki da da sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin jahar ta Adamawa baki daya.

Idris yace daman akwai hukumomin da gwamnatin tarayya ta kirkiro domin yaki da fataucin miyagun kwayoyi domin ganin an magance matsalar baki daya.

Shima anashi jawabi kwamishinan yan sandan jahar Adamawa C P Aliyu Adamu ya ce biyo bayan samamai da suke kaiwa a wurare daban daban ne dai yasa suka samu nasaran kama wadannan miyagun kwayoyi .

Don hakane suka mikaau ga hukumar dake yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi .

Kwamandan rundunan hukumar ta N D L E A Idris Muhammed Bello ya kirayi al umma da su kasance masu taimakawa hukumar ta su da wasu bayanai da zai basu damar magance matsalar baki daya.

Related posts

Leave a Comment