Rahoto Na Musamman Kan Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya

Ranar 21 ga watan Satumabar wannan shekara rana ce da majalisar dinkin duniya ta ware domin yin bikin ranar zaman lafiya a wani kokari na nemo mafita kan tashe-tashen hankula da ake fama da su na kabilanci da addini da sauran su a fadin duniya.

Sai dai bikin wannan rana na zuwa ne a dai dai lokacin da harkokin tsaro ke ?ara rincha?ewa a Najeriya inda ake zaman ?ar-?ar tsakanin ?abilu da addinai a ?asar gami da barazanar hare-hare daga ?ungiyoyin ?an ta’adda da kuma ?an bindjiga da ke kame mutane su na garkuwa da su.

Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri

A tarayyar Najeriya akwai yankunan da sun manta da samun zaman lafiya inda a kullum ake samun asarar rayuka sakamakon tashe-tashen hankula na addini da kabilanci da na neman iko ko neman mallakar wani kaso na tattalin arzikin kasa.

Wani rahoto da wata cibiar tsaro ta fitar a wannan watan ya nuna cewa a cikin watan Agusta da ya wuce an hallaka mutane 698 a sassan Najeriya.

Banda hare-hare ?an Boko Haram da ISWAP a shiyyar Arewa maso gashin Najeriya da ?an bindigar daji a yankin Arewa maso yammaci da tsakiyar Arewacin, ana kuma samun tashin-tashinar matsalar rashin tsaro da kabilanci da na addini a kusan dukkanin sassan ?asar.

Masana da masharhanta na bada irin na su dalilan da abin da ya hana a samu zaman lafiya a Najeriya tsawon lokaci.

Farfesa Khalifa Dikwa wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya ya ce hanyoyin da ya kamata a yi amfani da su domin wanzuwar zaman lafiya “Wajibi ne muzauna lafiya ba tare da nuna wariya ko ?abilanci a tsakaninmu ba, sabida a halin yanzu ?asar nan tana cikin wani halin ni ?a su” ina ji Dikwa.

Yayinda ake lalube na hanyoyin da za a samo bakin warware matsalolin da ke haifar da zaman lafiya masana da masharhanta gami da shugabannin al’aumma da na addini sun bada shawarwarin abin da ya kamata a yi.

Wani mazaunin birnin Maiduguri Safullahi Muhammad yace “Shawarata ga al’ummar mu shi ne mu yi hakuri muzauna da junanmu lafiya sannan mu dage da yin addu’a domin samun sa’ida sabida a wannan yanayin matsaloli da dama suna faruwa a cikin al’umma wadda hakan ya faru ne sakamakon halayen mu” inji Saifullahi.

Malam Isma’il Ibrahim Barnawi yace shawararsa ga al’ummar Najeriya shi ne ku kauda bambance da ke tsakaninmu mu rungumi zaman lafiya sabida nuna banbanci akidu da addini shima ya taka rawar gani na raba kan al’ummar ?asar nan.

“Musulmi da ?an uwanmu Kiristoci dukkanin mu mu yi karatun ta nutsu domin mu fahimci al?ibilarmu sabida sai da zaman lafiya ?asa za ta ci gaba” ina ji Isma’il Barnawi.

Shi kuma Fasto Yohanna Buru jakadan zaman lafiya na majalisar dinkin duniya ya bada ta sa shawarar da in an bi za a samu zaman lafiya.

Yayinda wasu da dama ke ganin ya zama dole a dakile hanyoyin da ake safarar haramtattun makamai da su ma wanzuwar su tsakanin al’umma na rura wutar akwai kuma masu ganin sai ana hukunta wa?anda aka samu da laifukan kunna wutar rikici in ana son samun zaman lafiya.

Related posts

Leave a Comment